Shahararren dan wasan kwallon kafa na Manchester City da Argentina Sergio Aguero ya cimma yarjejeniya da Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dake ƙasar Spaniya.
Kamar yadda jaridar Sport ta ruwaito dan wasan zai hade da Barcelona ne a ranar 1 ga watan Yulin gobe a yarjejeniyar zai shafe kaka biyu a Camp Nou.
Aguero wanda ya shafe sama da shekara goma a Barcelona zai sake hadewa da aminin sa Lionel Messi wanda da ma suna fafata wasa a matakin kasa, amma ba su taba maja a kungiya guda ba.
Kasarsa ta Argentina na daga cikin kanwa uwar gamin zuwansa Barcelona don hadewarsa da Messi ta hanyar zabtare albashin da za a rika biyansa.
Yanzu hala Aguero shine zai kasance lamba taran farko wa Barcelona, inda halin da Martin Braithwaite zai shiga ka iya ɗaiɗaita rayuwarsa ta kwallo, amma kuma yana da damar nuna bajintarsa.