Yayin da ake tsaka da tirka-tirkar rikicin sauay fasalin kasarnan da yan shiyar kudu ke yi, Shugaban Majalisar Dattijai Ahmad Lawan da na Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila sun dora alhakin fitinar kan gwamnonin yankin.
Shugabannin biyu suka ce abin bakin ciki ne da takaici a ce zababbun al’umma ne za su rika limancin irin wannan al’amarin da suka alakanta da na tsiya.
Ahmad Lawan ya ce Musababbin wutar rikicin matsalar tsaro dake ta kara ruruwa a kasarnan shine irin yadda aka yi watsi da harkar gudanar da kananan, wanda a ɓangaren Gbajabiamila ya ce ko da a ce ikirarin sauya fasalin kasar tana kan turba mai kyau, toh bai kamata a ce shugabannin siyasa da gwamnoni ne ke yi limanci ba.
Ya kara da cewa masu rajin sauya fasalin kasar kwata-kwata ba su bi ka’ida ba, kuma ba ta haka ake yi ba, kamata ya yi su nemo masu ruwa da tsaki don samo bakin zaren lamarin.
Duk wadannan kalamai da Shugabannin majalisar biyu ke yi, sun yi ne cikin hirarsu da manema labaran gidan gwamnati jim kadan bayan gudanar da Sallar Idi a Abuja.