Babbar Kungiyar Kwadago ta kasa ta bayyana cewa duk wanda ya kamo gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir el-Rufa’i ya kawo shi to lallai yana da wani babban tukwici da zai samo a sakamakon wannan babban aiki da ya yi na kama shi.
To da ma dai a jiya ne shi ma gwamnan Jihar el-Rufa’i ya sanar da makamanciyar wannan sanarwa kan shugaban kungiyar kwadagon Kwamared Ayuba Wabba, inda ya ce yana nemansa ruwa a jallo.
Idan za a iya tunawa dai a shekaran jiya ne Ƙungiyar NLC ta tsunduma wani yajin aikin gargadi na kwanaki biyar sakamakon wani abinda suk kira zalunci da gwamnan Kaduna Mallam Nasir el-Rufa’i ya yi na korar ma’aikata.
Cikin wata tattaunawa da BBC Hausa, Kakakin Ƙungiyar NLC Kwamared Nasir Kabir a yanzu hala uwar Ƙungiyar ta kasa ta shirya wani yajin aikin na gama gari a Najeriya biyo bayan wannan tataburza.
Wannan lamari na Jihar Kaduna dai ya kai ga Kungiyar Gwamnonin Arewa sun tsoma bakinsu ciki, inda suke kira ga bangarorin biyu da su kai zuciya nesa.
To sai dai NLC ta ce ba gudu ba ja da baya dangane da wannan yajin aiki da kuma zanga-zanga har sai el-Rufa’i ya sauya matakinsa na sallamar ma’aikatan Jihar.