• Lamarin ya afku ne a ranar Asabar din data gabata.
• Kullun Mijin sai ya bigi matar ta shi inji daya daga cikin yaran su.
• Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Runduanr Yan sandan jihar ta kama wani wani mutun mai shekara 45 ,mai suna Christopher, bisa zargin kashe matar shi sabida taki bashi naira 2,000 kachal.
Ana zarkin Christopher ne da yi wa matar shi mai shekara 39, dukan tashi kisha gishiri, a ranar Asabar din data gabata. a wani gida dake kan hanayar Agbontaen, na bayan makarantar sakandare ta Ebvareke , na birnin Benin.
Matar mai suna Isoken Christopher, da ake zargin mijin ta ya kashe ta, su na da Yara uku a zaman auren na su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yau Muhimbat da Hassan Giggs su ke cika shekara 13 da aura
Daya daga cikin yaran matar mai shekara 13 ya bayyana cewa, “Kullun Baban mu, idan ya dawo wajan aiki daga wata ma’aikata dake Benin, sai ya bigi Mahaifiyar mu.” Inji shi
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Edo,Bello Kontongs ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Comments 1