Yayin da wasu dalibai ke ci gaba da jiran sakamakon Jarabawar su ta shiga manyan makarantu wato JAMB, a hannu guda kuwa wasu na can na murna baki har kunne bayan ganin nasu sakamakon.
Toh sai da hausawa sun ce inda wani ya yi kuka to a nan wani ke dariya, domin bisa ga dukkan alamu dai sakamakon jarabawar na wasu ba ta yi musu dadi ba.
Wata kila ganin haka ne ya sa wani mai kayan sarki ya fito fili ɓaro-ɓaro ya kalubalanci daliban da kakarsu ta kasa yanke saka a wannan jarabawa.
Tun a makon da ya gabata ne dai dalibai da dama suka yi zaman dirshan don rubuta jarabawar, kuma ba tare da wata-wata ba hukumar ta JAMB ta saki sakamakon, lamarin da wasu ke farin ciki yayin da wasu kuma suka samu akasin haka.
Cikin wani faifan bidiyo da ke ta yawo a kafafen sada zumunta na zamani, an jiyo tare da ganin wannan mai kayan sarki zaune a kan kujera cikin wani ofishi tare da na’urar Laptop a gabansa yana kalubalantar daliban da suka fadi Jarabawar ta JAMB tare da kiransu da dakikai.
To da ma dai an ce gaskiya ɗaci gareta, wannan ne ya sa wannan kalamai na soja bai yi wa wasu matasa ko kuma daliban dadi ba bayan ganin wannan bidiyo, inda wasu ke ganin cewa duniya ce kurum ta yi mishi daɗi.
Sai dai ko ma menene, wannan soja ya kafa hujja da irin halin sakaci da daliban ke nunawa musamman yadda ya ce sun gaza maida hankalinsu kan karatu sai dai sharholiya kawai wacce ba za ta fishe su ba, inda yake cewa a wannan zamani za a iya samun matashi da tun bai gama sakandare ba amma ya iya daukar budurwa zuwa wurin shakatawa, lamarin da a ganinsa bai dace ba.
Daga bisani ya kuma kare hujjar tasa da cewa ita dai Jarabawar ta JAMB canki-canki ce da indai mutum ya yi karatu ya san abinda yake yi, to lashakka kawai dangwalawa zai yi ya samu garabasa.