Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kasa NEMA ta ce akalla gonaki 14,496 ne ambaliyar ruwa ta lalata a kananan hukumomi biyar na jihar Kano.
Babban Darakta na hukumar NEMA, Mustapha Ahmed Habib ne ya bayyana haka ga manema labarai yayin wani rangadin tantancewa da ya kai wasu al’ummomin da ambaliyar ruwan ta shafa a kananan hukumomin Warawa da Wudil na jihar.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Daraktan ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci hukumar da ta gudanar da tantance irin barnar da ambaliyar ruwan ta yi, sannan ya yi alkawarin tallafa wa wadanda abin ya shafa da kayayyakin agaji.
A cewarsa, kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Warawa, Wudil, Bebeji, Rano, da Dawakin Kudu.
KARANTA KUMA: Sama Da mutane 300 Ne Suka Mutu A 2022 – NEMA
“Wasu daga cikin al’ummomin sun hada da Warawa Gishiri Wuya gonaki 1,113, Larabar Gadon Sarki gonaki 1,135, Wudil gonaki 4,808, Bebeji gonaki 1,405, Rano gonaki 260, da karamar hukumar Dawakin Kudu gonaki 5,775 duk ambaliyar ta tafi dasu.
“Don haka ne muka zo nan tare da daukacin tawagar nan domin tantancewa. Amma abin takaici saboda yanayin hanya a wasu al’ummomin da abin ya shafa a karamar hukumar Warawa, ba mu iya shiga gonakin ba, saboda wasu motocin mu sun makale. Sai da muka koma wasu wurare a karamar hukumar Wudil,” inji shi.
Jarodar Daily Trust ta rawaito cewa, Ya kara da cewa za a hada rahoton tantancewar sannan kuma a mika shi ga ma’aikatar jin kai da kula da bala’o’i da ci gaban al’umma domin mikawa gaban Buhari.
Ya ce yayin da hukumar za ta samar da kayan agaji ga wadanda abin ya shafa, gwamnatin tarayya za ta sa baki cikin gaggawa tare da tallafa wa manoma ta yadda za su iya rake radadin asarar da suka yi.
A wani labarin kuma: An Yi Wa Gwamnan Jihar Benue Aikin Tiyata
Mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Terver Akase ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Larabar nan.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a ‘yan kwanakin da suka gabata kafafen sada zumunta sun yi yada rashin lafiyar Ortom sakamakon hotunan filastar bandeji a kansa.