Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya bi sahun yan Najeriya wajen juyayin mutuwar Hafsan Sojin Najeriya Laftanar Janar Ibrahim Attahiru wanda ya rasu sakamakon hatsarin Jirgin sama.
A Jiya ne Jirgin Attahiru ya yi hatsari tare da wasu mutane goma a hanyar su ta zuwa taro Kaduna daga Abuja.
“Muna taya yan Najeriya Juyayin Mutuwar Hafsan Sojin Najeriya wanda ya rasu a wani hatsari. Babu shakka rashinsa babban rashi ne ga Najeriya” Cewar Ofishin.
A bangaren Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana hatsarin a matsayin abin dubawa inda ya ce rayukan su ba zai tafi a banza ba.
Shi dai Attahiru an naɗa shi mukamin Hafsan Sojin ne bayan da Yusuf Tukur Buratai ya yi ritaya