Jami’an yan sanda a jihar Ogun sun kama wani tsoho Mai shekara 64, kuma mai suna Ayotunde Taiwo, bisa zargin yi wa wata yarin Yar shekara 2 fyade a garin Agbado, dake karamar hukumar Ifo dake jihar.
An kama wanda ake zargin bayan Kara da mahaifiyar yarinyar ta kai shi, a shalkwatar rundunar yan sanda dake Agbado a ranar Talata.
Mahaifiyar ya rinyar ta bayyana cewa, ta lura yarinyar ba ta iya ta fita dai dai, Wanda hakan ya sa ta yanke shawaran duba jikin ta.
A yunkurin hakanne yasa, Mai karar ta ce, Ta ga jini na guda ta al’aurar yarinyar.
Kazalika ta bayyana wa yan sanda cewa, da ta tabbayi yarinyar sai, ta nuna wani gida dake kallon na su.
Ma haifiyar yarinyar ta ce, ” Ko da na shiga gidan sai na ga Wanda ya yi aika aikan ya na wanke dan kanfanshi da ya jike da Jini, Wanda hakan ke nuna cewa shi ne yayi lalata da yarinyar” inji ta.
Har’ila yau Mai magana da yawun rundunar yan’sandan jihar Abimbola Oyeyomi, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a yau Talata, inda ya ce, bayan samun rahoton, jami’in dan sanda dake kula da yankin Agbado Kehinde Kuranga, ya tura da jami’an yan sanda yankin, inda suka kama mutumin a Gini mai lamba 11 dake hanyar Efon Alaaye na Unguwar Adiyan a garin Agbado.
Inda ya ce, yanzu haka, rundunar ta kai yarinyar asibiti, domin duba lafiyar shi.
Oyeyemi ya ce, Kwamishinan yan’sandan jihar Edward Awolowo Ajogun ya bada umarnin tura kundin bayanan Wanda ake zargi, ga Shashin bai wa iyalai kulawa, domin ci gaba da gudanar da bincike.
Comments 1