Kwanakin da suka wuce hukumar’yan Sanda ta kama jami’anta guda biyu da suka yi sanadin mutuwar wata matashiya mai suna Tina Ezekwe, to, a wannan karin ma hukumar ‘yan sanda reshen jihar Legas ta sake kama Isfekta Monday Gabriel, bisa zarginsa dake wajen mutuwar wani jami’in dan sanda.
Jami’in dan sandan yana kan wani aikin hadin-guiwa da sauran jami’an hukumar, a yayin da ya dinga harbi bai gaira ba dalili.
Sajan Felix Okago ya rasa ransa ne a yayin da yake bakin aikinsa, sannan wasu daga cikin jami’an sun raunta sakamakon harbin da aka musu.
https://dimokuradiyya.com.ng/fyade-yan-sanda-sun-kama-mutane-11-da-laifin-fyade/
A yayin da yake yunkurin tserewa Monday, ya dauki motar hukumar inda yake ya daki gadar dake yankin mainland.
Sai dai Shugaban hukumar’yan sanda na jihar Legas, ya bawa mataimakinsa umarnin cigaba da gudanar da bincike, sannan ya jajantawa iyalan mamacin, inda ya bayyana sa a matsayin jami’i nagari wanda ya mutu wajen kare kasarsa.