By Abbas Yakubu Yaura
An kama wasu mutane hudu sanye da kayan sojoji a jihar Osun bisa laifin fashi da makami.
Kwamishinan ‘yan sanda Olawale Olokode, wanda ya gabatar da wadanda ake zargin a karshen makon da ya gabata a Osogbo, ya ce uku daga cikin wadanda ake zargin David Agbebaku, Adewale Olubunmi da Oluwaseun Oderinde, an kama su ne bayan daya daga cikinsu wanda ya tsere daga soja ya samu Naira 300,000 da zamba daga hannun wani mutum.
DUBA WANNAN LABARIN: Osinbajo Ya Ziyarci Obasanjo Kwanaki Biyu Bayan Gudanar Da Taron Jam’iyyar APC
Olokode ya kuma ce wadanda ake zargin sun yi wa wani direba fashin motar sa kirar Honda Accord, wadda ake zargin sun sayar wa wani dila a Abeokuta dake jihar Ogun.
“Hakazalika,” in ji CP, “An kama wani sojan bogi mai shekaru 27, Ibrahim Ajibola, a kan titin Osogbo-Gbongan.”
“Kayan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da katin shaidar Sojoji guda hudu, hoton soja daya, lallausan satifiket na soja.
Sauran sun hada da tambarin sojan Najeriya, kayan kame kayan soja, mota kirar Honda mai lamba RGB399MB da EPE 509-GL, fom din sojoji ma lamba B.295 da kuma wukar jack, da sauransu.”
Ya kara da cewa ana gudanar da cikakken bincike kan lamarin kuma zasu fuskanci hukunci da zarar sun kammala bincike.
Comments 1