An kashe wasu ‘yan sanda da ba a tantance adadinsu ba a unguwar Enugwu-Ukwu da ke karamar hukumar Njikoka a jihar Anambra, yayin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai wa ayarin motocin Sanata Ifeanyi Ubah hari.
Majiyoyi sun ce ‘yan bindigar sun bude wa ayarin motocin wuta, kuma jami’an ‘yan sanda da ke cikin ayarin sun mayar da martani.
Karanta kuma: Sanata Ifeanyi Zai Fa fa ta a zaben gwamnan Anambra
Majiyar ta ce ta yiwu ‘yan bindigar sun bi Sanatan ne, amma babu wata shaida da ta tabbatar da hakan.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce an kashe ‘yan sanda shida a harin.
Jaridar DAILY POST ta kasa samun Sanata Ubah domin jin ta bakinsa saboda layin nasa ana amfani da shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Toochukwu Ikenga, ya tabbatar da cewa an kai hari kan jami’an rundunar a Enugwu-Ukwu, amma ya ce har yanzu ba a san adadin wadanda suka mutu ba.
Ya ce: “Eh, an kai hari a Enugwu-Ukwu a yau, amma ba a fayyace adadin wadanda suka mutu ba. Yayin da nake magana da ku, CP ya jagoranci tawaga zuwa wurin, kuma an dawo da zaman lafiya a yankin.
Ya yi alkawarin bayyana wa manema labarai sakamakon binciken da rundunar ta samu.
A wani labarin kuma: Kotu Ta Yi Sammacin Gwamnatin Tarayya Da ASUU Kan Yajin Aiki
Kotun masana’antu ta kasa, NIC, ta yi sammacin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, da su gurfana a gabanta a ranar Litinin a Abuja, kan yajin aikin da kungiyar ta shiga tsahon watanni takwas da suka gabata.
Wannan sammacin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ta yanke shawarar mika takaddamar da ta ki ci ta ki cinyewa a tsakaninta da ASUU ga kotun NIC.