By Abbas Yakubu Yaura
An samu tashin hankali a Ilesa a ranar Asabar bayan wani rikici da ya barke tsakanin kungiyoyin ‘yan banga dake garin Ilesa na jihar Osun.
Wasu majiyoyi da ba na hukuma ba sun ce an kashe mutane biyar yayin da wasu gungun ‘yan ta’adda suka yi artabu a yankuna daban-daban na garin.
A cewar wata majiya mai tushe daga jami’an tsaro da ba ta son a bayyana sunanta, tace rikicin ya faro ne a yankin Okutu Ope da ke Ilesa.
An ci gaba da samun labarin cewa wasu gungun ‘yan bindiga daban-daban guda biyu sun tunkari wani wurin gini domin sasantawa kafin a ci gaba da aiki.
Ya ce, “Bayan samun kudin, mambobin kungiyoyin biyu sun samu sabani a kan tsarin rabon kudin, kuma an kashe wani mamba mai suna ‘China’.
“Ya faru ne a yankin Okutu Ope ranar Juma’a. Daga baya jami’an ‘yan sanda suka iso suka tafi da gawar. Amma a ranar Asabar, an sake kashe wani dan kungiyar daya.
“Amma daga rahoton da na samu, wasu mazauna garin uku da ba su ji ba ba su gani ba, ciki har da wata mata da ta dawo daga coci, an kama su an sa su cikin wuta kuma aka kashe su. Rikicin yana haifar da tashin hankali a garin.”
Sai dai da aka nemi adadin wadanda suka mutu a hukumance, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Wale Olokode, zai ziyarci Ilesa domin tantancewa a nan take.