Rundunar tsaro ta farin kaya (DSS) a ranar Alhamis ta kama wasu bindigu da aka ɓoye a cikin buhunan doya a jihar Kano, sannan ta cafke wasu mutum biyu da ake zargi.
Waɗanda ake zargin suna kan hanyar su ne ta kai makaman zuwa inda aka shirya kai hari da su a ɗaya daga cikin jihohin Arewacin Najeriya, lokacin da aka cafke su. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Buni, Lawan Sun Taya Al’ummar Musulmi Murnar Sallah Karama
Kakakin rundunar, Peter Afunanya, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin tarayya Abuja, ya ce an kwace bindigogi biyu ƙirar AK-47 da kuma gidan harsashin AK-47 wanda babu komai a cikin sa.
Afunanya ya kuma ƙara da cewa wani babur ja ƙirar boxer da buhunan doya na daga cikin abubuwan da aka kwace a hannun waɗanda ake zargin..
Ya yi kira ga masu wajen shaƙatawa da wajen buɗe ido su ƙara tsaurara matakan tsaron su a lokacin bikin Sallah.
A kalamansa:
“Wannan abinda ya faru ya ƙara nuna bukatar mutane su ƙara sanya ido wajen kai rahoton duk wani abinda ba su yarda da shi ba jami’an tsaro mafi ya kusa da su.”
Shugaba Buhari Ya Umarci A Hukunta Jami’an Tsaro Dake Da Hannu A Sanar da Binani
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a binciki jami’an tsaro da ke da hannu wajen ayyana Sanata Aisha Dahiru, wacce aka fi sani da Binani, a matsayin zababbiyar gwamnan jihar Adamawa ba bisa ka’ida ba.
Tun da farko, Barista Hudu Yunusa Ari, Kwamishinan Zabe na Jihar Adamawa, ya ayyana Binani a matsayin wanda ta lashe zaben ba bisa ka’ida ba a lokacin da ba a gama tantancewa ba.
Comments 1