Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III ya tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal,Daily Post ta rawaito.
Wannan yana nuna kawo karshen azumin watan Ramadan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: An Ga Watan Idin Karamar Sallah a Ƙasar Saudiyya
Abubakar ya bayyana hakan ne a wani shiri kai tsaye a ranar Alhamis.
Ya ce ofishinsa ya samu bayanai kan ganin jinjrin watan domin kawo karshen azumin watan ramadana.
Ya ayyana Juma’a 21 ga watan Afrilu 2023 a matsayin ranar 1 ga watan Shawwal 1444.AH a Najeriya.
Sarkin Musulmin ya jinjina wa musulman Nijeriya tare da yi musu fatan Allah ya yi musu jagora da kuma albarka, inda ya bukace su da su ci gaba da yi wa kasa addu’ar samun zaman lafiya da ci gaban kasa.
A wani labarin kuma, Gwamna Buni, Lawan Sun Taya Al’ummar Musulmi Murnar Sallah Karama
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya roki Allah ya baiwa daukacin al’ummar musulmi da suka yi azumin watan Ramadan lada, kuma ya gafarta musu dukkan kurakurensu,Daily Post ta rawaito.
Gwamnan, a sakonsa na fatan alheri ga al’ummar Musulmi kan bikin Eid-el-fitr wanda ya kawo karshen azumin watan Ramadan, ya yi addu’ar Allah SWT ya saka wa kowa da kowa da ya yi azumin watan Ramadan, ya kuma gafarta masa kurakuransa.