- Mutane suna maido mana martani
- Wani babban mutum yayi barazanar kashe ni
- An sha yi min barazanar kisa
Shugaban EFCC, wato hukumar dake yaƙi da cin hanci da karɓar rashawa na ƙasa wato Abdulrashid Bawa ya bayyana cewa ana yawan yi masa barazan da rayuwar shi tun bayan da aka bashi shugabancin hukumar ta EFCC.
Bawa yace lallai mutanen da suke yaƙa bisa laifukan cin hanci suma suna maido da martani ta hanyoyi daban-daban. Shugaba Buhari ma ya taɓa yin irin wannan furuci a shekarar 2016.
Shugaban EFCC yayi wannan jawabi ne yau talata a hira da shi da aka yi a wani shiri na gidan talabijin ɗin Channels Tv.
Karanta wannan: Batun dakatar da Tuwita: An maka Gwamnatin Najeriya gaban kotun ECOWAS

Da aka tambaye shi ko yakan fuskanci barazana a yayin gudanar da ayyukan shi, sai ya kada baki yace: “Idan zaku iya tunawa naje birnin New York a satin da ya gabata. Wani babban mutum yake ce mun ya karɓi kiran waya daga wani mutum wanda binciken EFCC bai ma biyo ta kanshi ba, inda yake mishi iƙrarin cewa shi sai ya kashe shugaban EFCC wannan matashin yaron. Kamar yadda The Eagle ta wallafa.
“Ya jaddada mishi cewa ‘zan kashe shi, sai na kashe shi.’ wannan ne zai gwada maka yadda masu cin hanci ke nasu iya ƙoƙarin wajen gani bayanmu.”
Da aka tambaye shi kan cewa ko an taɓa mishi barazanar mutuwa, sai ya kada baki yace ‘eh, an taɓa mishi.’
A watan Fabrairun wannan shekarar ne dai shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar ta EFCC biyo bayan turka-turkar data janyo cire tsohon shugaban hukumar wato Ibrahim Magu.
A wani labarin kuma, sarkin Zazzau ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya koka yadda ayyukan ta’addacin ɓarayi ke ƙara ta’azzara a yankin musamman ma dai a cikin yan kwanakin.
Sarkin yace abun wanda babu wanda zaiyi fatan shigowarshi yankin ya riga da ya fara yin yawa, inda ya bayyana cewa yansu mazauna garin Zaria na rayuwa ciki tsoro da kuma shakku saboda ɓarayi da suke neman addabar yankin.
Idan baku manta ba, a ranar alhamis ɗin data gabata ne dai wasu ƴan bindiga suka kai hari a makarantar Nuhu Bamalli dake cikin garin Zaria inda suka kashe ɗalibi ɗaya tarr da yin awon gaba da wasu mutane goma ciki hada lakcarori guda biyu.