Tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar (PPA), Chief Peter Ameh, ya yi ikirarin cewa, hukuncin kotun koli kan zaben gwamnan jihar Ondo, shi ne jam’iyyar APC ba ta da dan takara a zaben gwamnan jihar Anambra da zai guda na a ranar daya gawatan watan Nuwamba shekarar nan
A wata sanarwa da ya fitar a Abuja, Sakataren Hadin gwiwar Jam’iyyun Siyasa CUPP na Kasa, ya kuma yi ikirarin cewa, tun da dai shugaban jam’iyyar APC na yanzu Mai Mala Buni, ya sanya hannu kan fom din takarar, ba tare da la’akari da hukuncin doka kan matsayin da yake akai na gwamna ba, to wannan fom din ya tashi a aikin banza, tamkar a zuba ruwa a cikin kogi.
“Ba zai iya rike mukamin Shugaban Jam’iyyar na kasa a matsayin zababben gwamna ba, don haka ko da APC ta yi nasara, za a iya soke zaben bisa dalilan da suka shafi sashi na 183 na Kundin Tsarin Mulkin Nigeria na 1999, kamar yadda aka yi wa dokar kwaskwarima”
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan fashi sun farmaki wani bankin a Ondo
“Duk abin da aka yi a karkashin shugabancinsa a yanzu, ya na bukatar amincewar dokar kasa ne, kuma ana iya juya shi a kotu bisa, hukuncin kotun koli da za’a yanke a yau.
“Kotun koli ta gano wata dabara kuma ta zata yi amfani da ita, don ceton jihar Ondo ga APC. a wannan shari’ar, har sai an yanke hukunci bisa cancanta ba tare da shigar Buni ba.”
“Hujjar ta kan wannan batun ita ce, ya sanya hannu kan wasu takardu da matakai, wadanda zasu kai ga sanya APC ta ka rawa a zaben Anambra da zai guda a ranar 6 ga watan Nuwamba.sashe na 183 ya bayyana komai bisa tsari.” A cewar shi.
“To an soke duk wata doka da ba ta dace da kundin tsarin mulkin Nigeria na 1999 ba, kamar yadda aka yi wa dokar kwaskwarima ”
“Abubuwan da kundin tsarin mulki ya tanada, suna da karfi a kan dukkan hukumomi da mutane a duk fadin tarayyar Nigeria,” in ji shi.