Wani bidiyo da aka sanya a manhajar TikTok ya nuna lokacin da wani ɗan Najeriya, ya yiwa matar da zai auri gwaji, inda ya gano cewa ashe ƴar hannu ce.
A ranar da budurwar zata zo otal ɗin, saurayin nata yana cikin ɗakin yana jiranta inda ya tsaya a matsayin wanda zai amfani da ita ya biyata kuɗi. Rahoton Legit.ng
KU KARANTA KUMA: Ku Zabi ‘Yan takarar Da Kuke So Ba Tare Da Tsoron Kowa Ba – Buhari ga ‘yan Najeriya
Mijin da zai aureta yayi takaici sosai lokacin da ya gano wacce zai aure na irin wannan baƙar sana’ar. Yace tuni har an sanya musu ranar aure a watan Afrilu.
Lokacin da budurwar ta iso otal ɗin ta fahimci cewa shiri akayi mata kuma asirinta ya tonu, sai ta kama balbalin bala’i tana ƙoƙarin faɗa da wanda ya kitsa shirin da akayi mata.
Ku kalli bidiyon a nan
Ga kaɗan daga cikin sharhin da mutane suka yi waɗanda Dimokuraɗiyya ta tattaro:
Sabie ya rubuta:
“Ina ganin laifin samarin da suke tunanin wai ba mace kuɗi zai sanya ta riƙe musu amana, idan mace bata da kamun kai da kawar da kai, kuna haɗuwa da ita, ka cika wandonka da iska.”
Your boyfriend atm holder ya rubuta:
“Tun lokacin da kuke soyayya baka gwada ta ba sai da kuka fara shirin aure. Baka da wayau.”
timidare602 ya rubuta:
“Lokacin da yayi mata gwajin ba shine abin lura ba, abin lura shine meyasa take karuwanci bayan tana cikin soyayya wacce zata kai ta ga aure…”
CNJ ya rubuta:
“Na sha faɗa, karuwa bata sauya hali.”
Yadda Aka Mamayi Wani Matashi Akai Masa Awon Gaba Da Mazakuta
A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya ga ta kansa bayan an yi masa awon gaba da mazakuta.
Wani mutum wanda ba a bayyana sunan sa ba ya shiga hannun jami’an tsaro bisa zargin satar mazakuta.
An dai cafke mutumin ne a birnin Owerri n jihar Imo, bayan an same shi da laifin mamayar wani mutum yayi masa awon gaba da mazakuta.