Fadar shugaban kasa ta ayyana cewa umarnin dakatar shafin tuwita a Najeriya ba wai an yi shi ne saboda shafin ya goge rubutun shugaban kasa Muhammadu Buhari kadai ba.
Wata sanarwa da Kakakin Shugaba Buhari ya fitar Mallam Garba Shehu, ta ce shafin ya jima yana yaɗa labaran karya da ka iya tada tarzoma tsakanin yan kasa.
Fadar shugaban kasar ta ce an daɗe ana ɗaga kafa wa kamfanin amma bai daddara ba, wannan ne ya sa aka ɗauki matakin hana ayyukansa a Najeriya.
Ko da yake Sanarwar ta nuna rashin jin daɗin fadar shugaban kasar bisa matakin na tuwita, amma ta ce babu nasaba ta kusa tsakanin goge rubutun Buhari da dakatarwar.