Tawagar kungiyar dake rajin kafa kasar Oduduwa ta Yarbawa karkashin shugabancin Sunday Igboho ta yi sansani a birnin Ado Ekiti don gudanar da zanga-zanga a yau Asabar.
Da yake jawabi yayin zanga-zangar, Sunday Igboho ya ce tuni suka fara cimma burinsu na korar Fulani daga yankin Yarbawa, inda ya ce maganar zaɓe a yankin ma babu ita a 2023.
Ko da yake Igboho bai halarci taron a kan lokaci ba, amma hakan bai hana dandazon yan Oduduwan yi masa tarba ta girma ba.
Ya kuma ce Yarbawa ba za su zama bayin Najeriya ba, don hala dole ne sai sun kwato ƴancin kasar su.