Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa ba zai bar ragamar mulkin Najeriya hannun wanda ko yankinsa ba ya iya lashe zabe ba.
Shugaba Buhari ya yi wannan alwashi a ranar asabar yayin kaddamar da wata gidauniyar zaman lafiya mai suna Kudirat Abiola Sabon Gari Peace Foundation a Kaduna garin gwamnan.
Shugaba Buhari wanda ya ce yanzu haka babu wani abu da yan Najeriya ke bukata sama da zaman lafiya, ya ce zaman kasar tsintsiya madaurin guda, shine zai kara tabbatar da zaman lafiyarta ba wai wargajewa ba.
Shugaba Buhari ya ce wadannan tsiraru dake rajin kafa sabuwar kasar, suna yi ne kawai cikin duhun kai, domin ba su san menene yaki ba.
Buhari wanda Babban Sakataren Hukumar tattara kudaden shiga da tsara su Alhaji Muhammad Bello Shehu ya wakilta, ya kara tabbatar da cewa indai kuma jama’a na buƙatar zaman lafiya ya ɗore, to dole ne su ma su tashi tsaye su dukufa kan nagartattun ayyuka.
“Zan kara nanatawa, wadannan yara dake rajin sauya fasalin kasa, idan na tambaye ku, menene kuke son sauya fasalinta a ciki? Idan ka tambayi galibinsu ba su san menene za su faɗa ba”
“Wasun su ma ba su san menene cikin kundin tsarin mulkin 1999 ba, galibin abinda ke cikin kundin tsarin mulkin 1999 shine ke cikin na 1979” Cewar Shugaba Buhari.