
Jaridar Tvcnews ta wallafa Yan sanda sun damke wata budurwa da tayi karyar an sace ta kuma ta bukaci 500,000 kudin fansa
Yan sandar Jihar Ekiti sun damke wata budurwa mai suna Abimbola Suluka tare saurayinta Oluwaseu Olajide bayan tayi karyar sace ta.
Abutu Sunday mai magana da yawun Yan sanda yace ” kanwar Abimbola ta kawo rahoto cewar Yayarta ta ba’a ganta ba tun bayan tafiyar ta makaranta.
KARANTA:- Haryanzu ana cigaba da fafatawa waje ceto Yaran da aka sace a Kebbi
Kamar yadda Abutu yace ” a lokacin da aka kira wayar Abimbola wani wanda ba’a sani ba ya dauki wayar” yace ke cewa ” a halin yazu sun dauke ta bazamu sake ta ba har sai an biya kudin fansa dubu dari biyar.”
Da aka biya kudin ta hanyar wani asusun baki sai Yan sanda suka bi diddigin suka kamo mai asusu. Yan sanda suka tilasta mashi daya jagorance su har inda wannan yake, Inda ya kaisu wani dakin kwane dake babban birnin jahar.
Lokacin da ake zantawa da Abimbola cewa tayi ” ita tayi nufin data nema ma iyalanta kudi ne domin bada damar komawa kasar Ikiti don cigaba da karatun ta na zama likita.”
Comments 1