
Haryanzu ana cigaba da fafatawa waje ceto Yaran da aka sace a Kebbi
Jaridar Thisday ta ruwaito cewar “Ana cigaba da bin diddigin Yaran da aka kwashe a Makarantar Yawuri dake Jihar Kebbi”.
A sati daya wuce ne sama da dalibai tamanin Yan bindiga suka kwashe a garin Yawuri dake Jihar Kebbi wanda mafiya yawan su Mata ne da Malamai Biyar.
KARANTA:- Yan bindiga sun Kai Hari a wasu Kauyuka dake Jihar Neja
Wani masanin abun da ke aukuwa akan lamarin ya baiwa Jaridar Thisday labari ” wasu daga cikin daliban da aka sace an dawo dasu”
Acewar sa sauran Yaran Yan bindigan sun raba su gida biyar ne wanda yanzu hakan Sojoji sun zagaye su.
Sojojin dai ba suyi ta harbe harbe ba saboda kada a kashe Yaran ko Yan bindigan su harbe su.
Mai bada labarin yace ” sun dai zagaye su sun tattaunawa tayyada zasu kubutar dasu ba tare da an kashe Yaran ko guda ba.”
KU kansance tare damu domin jin yadda lamarin ke aukuwa.
A WANI LABARIN:- GwnamnanJihar Kebbi Alhaji Atiku Abubakar Bagudu ya ce zai shiga daji tare da mafarauta don ceto ɗaliban da aka sace na makarantar sakandaren Birnin Yauri dake karamar hukumar Ngaski ta Jihar.
Bagudu wannda shine Shugaban Ƙungiyar ci gaban gwamnoni ya yi wannan ikirari ne yayin da maharban jihar suka kai masa ziyara.
Kazalika kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN ya labarto cewa, baya ga kungiyar maharban ita ma ƙungiyar gwamnonin Najeriya karkashin shugabanta Kayode Fayemi kuma Gwamnan Jihar Ekiti ta kai wa Gwamnan ziyarar jajantawa.
Bagudu ya tabbatar da cewa ba shi kaɗai ba, karin wasu gwamnonin za su rufa mishi baya wajen dunguma zuwa daji don ceto daliban.
Ya kara da cewa ba kuma za su yi hakan ne gaba gaɗi ba, sai sun tattauna da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki don gudun kawo katsalandan ga harkar ceto ɗaliban.
Ya ce “Toh, kamar yadda na alkawarta muku, za mu fito mu dunguma zuwa dajin tare, kuma ranar da za a tafi ba zan je ofis ba”
Bagudu ya bayyana cewa indai dubban jama’a za su fito su ui gangami yayin yakin neman zabe, to bai ga dalilin da zai sa su ma a saka musu ba a daidai wannan lokaci
Comments 1