Shugaba Muhammadu Buhari yace , idan har nahiyar Afirka na son yarjejeniyar cinikayya ba tare da shinge ba a nahiyar ta yi tasiri sosai wurin zuba jari na anan gaba a fannonin da suka dace, dole ne gwamnatocin nahiyar su samar da manufofin tallafawa da suka dace, tare da samar da ababen more rayuwa da tabbatar da samar da kwararrun ma’aikata.
Vanguard ta ruwaito cewa, Buhari ya bayyana hakan ne a saƙon sa na a wurin buɗe taron ranar masu fitar da kayyaki ta ruwa karo na tara da ya gudana a Lagos.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan Najeriya Miliyan 25 Na Fuskantar Barazanar Yunwa — UNICEF
Buhari wanda ƙaramin Ministan Sufuri Ademola Adegoroye ya waƙilta, yace akwai buƙatar shugabanin a nahiyar Afirka su samar da ayyukanyi masu inganci , tare da samar da ayyukan, haɗi da ƙarfafa mata da samar da abinci tare da rage rashin dai daito.
Ya kara da cewa, sake fasalin yarjejeniyar ciniki cinikayya a nahiyar Afirka zai kara yawan kayayyakin da Najeriya ke fitarwa zuwa sauran yankuna dake, wajen yammacin Afirka.
Haka kuma ya bukaci kasashen Afirka da su fadada tare da ba da gudummawarsu a harkokin cinikayyar kasa da kasa domin ɗaga darajar kasuwanci duniya, don samar da wadata da bunkasa tattalin arzikinsu.
Ya ce gwamnatin Najeriya ta kara himma da nufin gano sabbin damammaki na banbance-banbance da bunkasa kasuwanci a karkashin shirin AfCFTA da sauran matakan da ake ganin ya dace don shawo kan matsalolin da ake fama da su na kasuwanci tsakanin kasashen Afirka.
A wani labarin kuma, Malaman Birtaniya Da Wales Sun Sanar Da Shiga Yajin Aiki
Ana shirye shiryen fara yajin aiki a Birtaniya, babbar ƙungiyar Malamai ta ƙasar ta sanar da cewa zata shiga yajin aiki saboda matsalar albashi a Ingila da Wales. Kamar yadda BBc ta ruwaito.
Haɗadiyar ƙungiyar harakokin ilimin ƙasar (NEU) tace mambobin ta sun amince da su gudanar da tattaki a matsayin hanyar kiraye kiraye ga hukumomi akan tashin farashin kayyaki.