Shugaban Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Joan Laporte ya fito fili ya bayyana matsayar kungiyar kan makomar dan wasanta Lionel Messi.
Laporta wanda ke bayani wa manema labarai a yau juma’a yace a yanzu haka tattaunawa tsakanin bangarorin biyu ta yi nisa to saidai akwai wani hanzari ba gudu, domin har yanzu babu wata matsaya dangane da makomar Lionel Messi a kungiyar.
Kungiyar da a wuya take ta ga dan wasan ya ci gaba da zama a Barcelona, to amma kuma ana ganin lamarin sa idan ya yi tsami to fa zai iya tafiya a matsayin kyauta.