Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce dole ne jam’iyyun siyasar kasar nan su bayyana hanyoyin da suka samu kudaden yakin neman zabensu tare da kiyaye ka’idojin da suka shafi kudaden yakin neman zabe da kayyade kashe kudade.
Shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a wata hira ta musamman da yayi da gidan talabijin na Trust TV.
A cewarsa, akwai kuma iyaka ga abin da daidaikun mutane za su iya ba da gudummawar don ba da kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe, saboda daidaikun mutane ba za su iya ba da gudummawa kawai ba bisa ƙayyadaddun iyaka.
KARANTA ANAN: Wata Babbar Ɓaraka Na Neman Kunno Kai Tsakanin Tinubu Da Wasu Jiga Jigan APC
“Jam’iyya kuma tana da nata iyaka dangane da abin da za ta iya kashewa da suka hada da inda kudaden ke fitowa da alhakin bayyana cikakken bayani kan gaskiya, da kiyaye iyakokin doka na zahiri.”
Shugaban na INEC ya nanata cewa jam’iyyu ba za su iya samun gudunmawar kudi daga wajen kasar nan ba, kuma idan akwai kudaden da wata jam’iyya ta karba daga wajen kasar nan, to sai an mika wa hukumar.
Dangane da batun tsaro ta intanet da na’urorin lantarki, Yakubu ya ba da tabbacin cewa hukumar za ta zuba jari mai tsoka a kan harkar tsaro ta yanar gizo, inda ya kara da cewa “Duk wata kungiya da ke gudanar da harkokin sadarwa ta yanar gizo tana da saukin kamuwa da kutse amma tsarin tsaron mu yana da karfi sosai.”
”Kuma na tabbata ko da bamu fito a gidan talabijin na kasa mu fadi ainihin yadda za mu kare tsarinmu ba, amma mun gamsu cewa tsarin tsaron mu yana da karfi.”
A wani labarin kuma: Najeriya Na Bukatar ‘’Yanci Daga Ta’addanci Da Talauci – Sanwo-Olu
Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas a ranar Asabar ya ce ko bayan shekaru 62 da samun ‘yancin kai, Najeriya na ci gaba da kokarin samun ‘yanci daga ayyukan ta’addanci da talauci.
Sanwo-Olu ya bayyana haka ne a yayin faretin zagayowar ranar samun ‘yancin kai, domin tunawa da ranar samun ‘yancin kai na tarayyar Najeriya karo na 62.
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta jihar Legas ce ta shirya faretin da aka gudanar a filin wasa na Mobolaji Johnson Arena dake Onikan.