- Muna da isassun kayan aiki da zamu taimaka dasu
- Muna kashe £70,000 wajen jigilar kuɗaɗe
- Ba sai kunje ƙasashen turai ba don buga kuɗi
Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele yace bankin yana son taimaka ma babban bankin ƙasar Gambia wajen fito da sababbin kuɗaɗe.
Emefiele ya bayyana hakan ne ranar talata a yayin wata ziyara ta kwana biyu da shugaban babban bankin ƙasar ta Gambia Buah Saidy yare da muƙarrabansa suka kawo masa.
Yayi wannan jawabi ne bayan roƙon da babban bankin Gambia yayi kan ganin an taimaka musu wajen magance matsalar karancin kuɗaɗe da suke fuskanta kamar yadda jaridar Punch ta wallafa.
Karanta wannan: Ina goyon bayan sauya fasalin kasar nan dari bisa dari: Cewar Gwamna Fintiri
Saidy ya faɗa ma gwamnan babban bankin Najeriya cewa, dogaro da suke akan injin buga kuɗin su wato De La Rue na birnin London yayi tsada da yawa kuma ba zasu iya cigaba da ɗawainiyar hakan ba.
Yace suna kashe aƙalla fan dubu sabai’in, £70,000, domin jigilar kuɗaɗen su da aka buga daga ƙasar Sri Lanka zuwa ƙasar ta Gambia.
Gwamnan babban bankin Najeriya ya tabbatar musu da cewar zasu iya samar ma da ƙasar ta Gambiya isassun kuɗaɗe masu tsaro maimakon ace sai sunje kashashen turai domin a buga musu sababbin kuɗaɗe.
A wani labarin kunji cewa babban jigo a cikin jam’iyyar APC mai mulki kuma tsohon gwamnan jihar Lagos, Asiwaju Bola Tinubu yayi dawowar bazata zuwa Najeriya ana tsakiyar yaɗa jita-jitar cewa ya mutu.
Dailytrust ta wallafa cewa masu yaɗa labarin mutuwar ta Bola Tinubu dai suna cewa wai ya mutu ne a sakamakon wata rashin lafiya da yake kan yi ma magani a ƙasar waje.
Labarin ya dauki hankali matuƙa, musamman ma dai a shafukan sada zumunta na zamani inda jama’a da dama sukai ta tofa albarkacin bakunan su.