Gwamnatin jihar Kano ta ƙalubalanci wasu cikin dattawan Kano kan matakin da suka ɗauka na kai wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ƙorafi kan batun ƙarɓo bashi da gwamnatin Kano ke shirin yin daga ƙasar China.
Kwamishinan raya karkara na Kano Musa Iliyasu Kwankwaso shi ne ya bayyana hakan ta cikin shirin ‘Kowane Gauta’ na rediyo Freedom dake bada damar faɗin albarkacin baki.
Kwamishinan ya ce “ku ma janye maganar cewa dattawan jihar Kano ne su ka kai ƙorafin, don kuwa dattawan kwankwasiyya ne kaɗai”.
Musa Ilyasu ya zargi dattawan da yunƙurin hana ci gaban jihar Kano, inda ya ce gwamnati ta tattauna da masana kan batun ciyo bashin domin kuwa abu ne da zai kawo wa Kano ci gaba tare da farfaɗo da tattalin arzikin jihar dama ƙasa baki daya.