Kwana guda bayan kisan tsohon mai baiwa Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa Ahmad Gulak, a yanzu haka an sake gano gawar wani sojan sama da ake zargin ƴaƴan Ƙungiyar Inyamurai ta IPOB da hallakawa a birnin Owerri fadar gwamnatin Jihar Imo.
Jaridar Shahara Reporters ta ruwaito cewa an hallaka jami’in Sojin ne mai suna Eberechukwu Emereuwa daidai lokacin da umarnin ci gaba da zama a gida na Kungiyar IPOB ke ci gaba aiki.
Ko da yake har yanzu ba a gano makasan sojin ba, amma ana alakanta lamarin ne kan ƴan Ƙungiyar Inyamurai masu raji kafa kasar Biafra wato IPOB.
Kazalika duk a ranar asabar din da ta gabata, wasu yan bindiga da ake zargin yan IPOB din ne sun hallaka sojoji biyar a garin Ihiala dake karamar hukumar Ihiala duk dai a jihar ta Imo.
Yanzu haka lamarin harin dauki ɗaiɗai na ci gana da karuwa a yankin kudu na kasar nan, al’amarin da ake ta alakanta shi da hare-haren ƴan Ƙungiyar masu rajin samun kasar Biafra.