Gwamnan Jihar Cross River Ben Ayade ya sanar da matakin sallamar wasu kwamishinoninsa guda hudu a yau Litinin.
Sanarwar ta fito ne dauke da sa hannun Babban Mai baiwa gwamnan shawara kan kan kafafen yada labarai Mista Christian Ita a da aka rabawa manema labarai a birnin Kalaba fadar gwamnatin Jihar ta Cross River.
Kwamishionin da aka sallamar sun hada Mike Usibe da Rita Ayim da Ntufam Etim gami da Asu Okang.
Kuma tuni aka umarce su da su gaggauta maido da kadarorin gwamnati dake hannun su nan take.
Idan za a iya tunawa a ranar 20 ga watan Mayun nan ne gwamna Ayade ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.