Wani matashi ɗan Najeriya ya bayyana yadda budurwar da ya gama ɗawainiya da ita na tsawon shekara huɗu ta rabu da shi.
Ɗan Najeriyan ya bayyana hakan ne a wani rubutu da wani mai amfani da sunan @Sealveeyah2 Twitter, ya wallafa. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Matakin CBN Na Kin Karɓar Tsohon Kudi Tamkar Cin Fuska Ne Ga Kotun Koli – Lauyoyi
Ya bayyana cewa a lokacin da suke rare da budurwar ta sa, duk bayan kwana biyu sai ya tura mata kuɗi sannan dum wata ɗawainiyarta a kansa take.
Ba iya nan kawai ya tsaya ba, shine kuma ya ɗauki nauyin biyan kuɗin makarantar ɗan’uwanta. Saurayin ya bayyana cewa duk da sadaukarwar da yayi mata, sai da ta rabu da shi.
Yace ya dandara ba zai taɓa ƙara yin soyayya ba a rayuwar sa.
Ƴan Najeriya da dama sun bayyana ra’ayoyi daban-daban kan wannan labarin na sa mai sosa zuciya.
Da yawa daga cikin sun fusata bayan da @Sealveeyah2 ya rubuta:
“Tun da har yanzu abun yana cikin ranka, ya nuna cewa har yanzu baka manta da tunanin ta ba.”
Ga kaɗan daga cikin waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
@Jofortan1 ya rubuta:
“Meyasa bata kawar da zuciyar ta ba lokacin da tayi masa wannan ɗanyen aikin, kawai sai ya manta ko? Saboda ba ɗan’uwanka ba ne ko?”
@abmillz ya rubuta:
“Idan ka isa ka manta da komai bayan ka gama ɗawainiya da wata tare da biyan kuɗin karatun ƙaninta. Idan ka isa kayi!”
@iamBawzCartel ya rubuta:
“Na tabbatar da ace ɗan’uwanka ne ba zaka faɗi wannan shirmen ba. Idan da sauƙi kai kayi mana sannan a rabu da kai.”
So Kenan: Kyakkyawar Budurwa Ta Auri Gurgu, Sun Samu Ƙaruwar Ɗiya Mace
A wani labarin na daban kuma, bidiyon wata kyakkyawar budurwa da ta auri gurgu ya ɗauki hankula sosai.
Mutane sun cika da mamaki bayan bayyanar bidiyon wata kyakkyawar budurwa da ta auri wani saurayi gurgu.
Bidiyon wanda wani mai amfani da sunan @theclements2020 ya sanya a TikTok, ya nuna cewa ma’auratan biyu anyi musu baiko ne a shekarar 2021 bayan sun kamu da ƙaunar junan su.