Ɗalibai 2 mata da aka sace na jami’ar tarayya da ke a Gusau, jihar Zamfara, sun shaƙi iskar ƴanci.
Ɗaliban sun samu ƴanci ne bayan kwashe kwana 12 a hannun masu garkuwa da mutane. Rahoton jaridar Vanguard
An dai sace ɗaliban ne bayan wasu mutane ɗauke da bindigu sun afka musu a gidan su da ke a unguwar Sabon Gida.
KU KARANTA KUMA: Rashin Imani: Mijina Yana Lakadamun Dukan Tsiya dani Da Mahaifina — Mata Aure
Ƙungiyar ɗaliban jihar Zamfara, ta tabbatar da sakin ɗaliban, sai dai ƙungiyar ba ta bayyana cewa ko an biya kuɗin fansa ba.
Kakakin ƙungiyar, Umar Abubakar, ya taya hukumomin makarantar da iyayen ɗaliban murna waɗanda suka shiga cikin tashin hankali bayan an sace ɗaliban.
A kalamansa:
“Mun yaba sosai bisa jajircewar da hukumar makaranta ta yi wajen ƙoƙarin ganin an sako ɗaliban.
“Mun yaba da ƙwarewa, sadaukarwa da ƙoƙarin da jami’an tsaron mu suka yi wanda ya taimaka sosai wajen sako daliɓan.”
“Mun kuma yaba da ƙoƙarin da ƴan’uwan mu ɗalibai suka yi da addu’o’i, da sauran ƙingiyoyi bisa haɗin kan da suka bamu da taimakon su domin ganin ɗaliban sun samu ƴanci.”
“Muna kira ga jami’an tsaro da su tabbatar cewa an cafke tare da gurfanar da duk masu hannu a cikin rashin imanin da aka yi, duk tsawon lokacin da zai kwashe, sannan su tabbatar cewa hakan bai ƙara aukuwa ba akan ɗaliban mu.”
Anyi Babban Rashi, Tsohon Dan Wasan Najeriya Ya Kwanta Dama
A wani labarin na daban kuma, tsohon ɗan wasan Najeriya na tawagar Super Eagles ya riga mu gidan gaskiya.
Tsohon ɗan wasan tsakiya na Super Eagles, Emmanuel Ebiede, ya mutu a ranar Juma’a a birnin Port Harcourt, na jihar bayan ya yi fama da matsalar kumburin hanta.
Ebiede, mai shekara 47, a duniya mutu ne da misalin ƙarfe 4 na yamma a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Rivers.