Wata kotun Kwastamari da ke Mapo, Ibadan, Jihar Oyo ta dage ci gaba da zamanta har zuwa ranar 6 ga watan Yuni domin yanke hukunci kan karar da wata mata, Tawakalitu Hassan ta shigar a gabanta kan mijinta, Ganiyu Hassan wanda ta zarge shi da rashin gaskiya da kuma cin zarafi akai-akai,kamar yadda Tribune Online ta rahoto.
Mai shigar da karar ta bayyana cewa wanda ake tuhumar baya saurara mata alokacin da yake lakada mata dukan tsiya, amma kuma bayan haka yana yayyaga mata tufafi ya barta tsirara.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben Kano: ‘Yan Sanda Sun Sanya Dokar Hana Zirga-zirgar Ababen Hawa
Tawakalitu ta ci gaba da cewa, mijin nata ya lalata mata sana’o’in ta ne sakamakon rashin rikon sakainar kashi da yake yi mata.
Mai shigar da karar ta shaida wa kotun cewa tana son wanda ake kara ya fita daga rayuwarta, don haka tana rokon mai shari’a kan daya raba auren kuma ya bata damar rikon ‘ya’yansu biyu cikin hudu.
Sai dai kuma Mijin nata, Ganiyu ya amince a tsinke igiyar auren kan cewa shi ma baya sha’awar aurensu domin matarsa ‘yar iska ce.
Ya roki kotun da ta ba shi kulawar ‘ya’yansu hudu da a halin yanzu ke hannun sa saboda matarsa bata da kyau ba abin koyi a gare su ba ce.
Tawakalitu da ke ba da shaida ta ce, “Na fara zama da mijina ne bayan ya yi min ciki a lokacin da muke soyayya.
“Bai dauki wata kyauta ya baiwa iyayena ba,haka kuma bai biya kudin sadaki na ba.
“Ganiyu yana yawa dukana tun farkon aurenmu,Bai gamsu da duk abin da na yi ba kuma yana ta gunaguni da ihu a kaina.
“Na bar shi na koma gidan iyayena bayan mun haifi ’ya ta biyu saboda ya ki cewa na huta.
“Ya zo ya roke ni kuma na amince in koma wurinsa bayan na yi tunani sosai.
“Mun sake haifar wasu ’ya’ya biyu bayan na dawo gidan sa da aure, amma Ganiyu maimakon a samu canji sai ya kara tsananta mun.
“Bai tsaya iya lakadamun duka ba har ma yana yaga tufafina, ya bar ni tsirara a gaban yaranmu da makwabta.
“Mijina ba ya wurin ’ya’yanmu. Bai san yadda suka kasancewa ba kuma bai kula da iliminsu.
“Na kasance ina ciyar da gida kuma ina biyan kowace bukata domin mijina baya ba da mafi yawan nauyin da ya rataya a wuyansa na ciyar da ni.
“Ya lalata kasuwancina ne sakamakon rashin salon rayuwar sa kuma na bayyana rayuwa daga hannu zuwa baki.
“Na sake barin gidansa a karo na biyu da alkawarin ba zan dawo ba saboda ya zamarwa rayuwata matsal.
“Ya Mai Shari’a, Ganiyu ya taka daurinsa a ranar da ya yi wa mahaifina dukan tsiya bayan an raba ni da shi.
“Mijina ba shi da tausayi. Ba zan iya zama a ƙarƙashin rufi ɗaya tare da shi ba.
“Saboda haka, na roki wannan kotu mai albarka ta dakatar da dangantakarmu, ta ba ni kulawar yara biyu cikin hudu, yayin da yake da ‘yancin kai musu ziyara a ranar Lahadi.
“Ina rokon kotu da ta sanya shi alhakin kula da su.”
Ganiyu ya amsa ya ce, “Ya mai shari’a, matata ba ta da kunya. Tawakalitu ta isa ta bani kunya. Ni, don haka, ina goyon bayan warware aurenmu.
“Matata maƙaryaciya ce. Ta koma tare da ni bayan mun gudanar da bikin gabatarwa na biya mata sadaki.
“Hanyar rayuwar Tawakalitu ta sabawa ta mace saliha. Ta kasa zama misali mai kyau ga yaranmu.
“Matata ta mayar da ni abin ba’a a unguwarmu sakamakon rashin mutuncin da take yi.
“Ta jawo min kunya da iyalina gaba daya. Ni yanzu ina zagawa tare da sunkuyar da kaina.
“Yan kungiyar OPC ne suka ja Tawakalitu gida da daddare.
“A cewarsu, sun kama ta da wani mutum suna ta soyayya a cikin wata makarantar da ke kusa da gidanmu.
“Ta fita daga gidana ne bayan faruwar lamarin, domin a fili yake cewa aurenmu ya zo karshe.
“Ya Mai Shari’a, ina rokon abani kulawar dukan ’ya’yanmu, domin ta sami damar zuwa gare su a duk lokacin da ta ga dama.
“Ta bar su tare da ni lokacin da za ta tafi kuma zan kula da su sosai.
“Tawakalitu za ta bata ‘ya’yanmu idan an bar su a hannunta. Za su yi rayuwa mafi muni fiye da tata.”
Shugabar kotun, Mrs S.M Akintayo, bayan ta saurari bangarorin biyu, ta dage cigaba da sauraron karar.
A wani labarin kuma, Abun Ayaba: Daraktan Yakin Neman Zaben Tinubu Ya Mayar da Rarar Miliyan N2.4m
Daraktan Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na Tinubu-Shettima na ‘yan kasashen Prince Ade Omole, ya mayarwa kwamitin Naira miliyan N2.4m.
Kudaden dai sun kasance ma’auni ne na asusun yakin neman zabe na naira miliyan N10m na farko da aka raba wa tawagar ‘yan kasashen waje kan tunkarar zaben shugaban kasa na 2023.
Comments 1