Wani mai wa’azin bakin titi ya bayyana yadda wani mai yankar aljihu da ke Accra a kasar Ghana ya mayar da watsar da ya sata daga wani, YEN.com.gh ta ruwaito.
A wani bidiyo da aka wallafa a TikTok, mai wa’azin ya ce barawon ya saurari wa’azinsa ne inda daga nan imani ya shige shi ya yanke shawarar dena sata.
KU KARANTA: Batagari sun ƙone ɓarawon waya jahar Bayelsa
An bukaci mai wayar ya zagayo zuwa wurin mai wa’azin don ya gabatar da kansa a gane cewa wayar ta shi ce sannan ya amsa.
Mai wa’azin wanda yake kokarin ganin kowa ya dawo tafarkin biyayya ga mahalicci ya ja hankalin jama’a da dama da ke yanar gizo.
A bidiyon wanda Yen.com.gh ta gani a TikTok, wani fitaccen mai wa’azi a bakin hanya, @suportsofsuronyame ya ce barawon ya je har wurinsa inda ya bayyana masa cewa ya Saco wayar wani amma yana so ya mayar.
Matashin mai wa’azin ya bayyana cewa ya saci waya kirar IPhone 11 Pro Max ne daga baya ya gane cewa ya tafka babban kuskure.
Hakan yasa mai wa’azin ya bukaci cewa duk wanda ya san ya nemi wayarsa ya rasa mai irin wannan kirar, ya yi gaggawar zuwa gare shi don gabatar da kansa.
‘Yan Ghana da dama sun yaba da shi inda suka dinga yi masa addu’a tare da fatan alkhairi akan wannan namijin kokarin da ya yi.
Kawo yanzu, bidiyon ya samu masu jinjina sama da 32,000 da kuwa sharhi daban-daban fiye da 600.
An yi ram da ɓarawon da yaje satar jannareto a kotu ana shirin shari’a
Mutane da dama sun yi mamakin yadda wani barawo ya samu kwarin gwiwar yin sata a wata kotu dake jihar Ogun, Legit.ng ta ruwaito.
Matashin ya samu damar dan hutun amsar katinan zabe da aka yi inda ya balle ya shiga kotu yayin da ya yi yunkurin sace jannareto.
An kama Folorunsho Olaniyan yayin da yake satar a kotun da ke Ado-Oda da ke karamar hukumar Ota da ke Jihar Ogun.