Wani matashi ɗan Najeriya ya fasa asusun da ya kwashe shekara biyu yana tara kuɗaɗen sa a ciki.
Matashin mai amfani da @sirprosper4e a manhajar TikTok, ya fasa asusun ne yayin da wa’adin tsofaffin kuɗi yaƙe ƙara gabatowa. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Rayuwa Kenan: Allah ya yiwa wata amarya rasuwa kwanaki kaɗan bayan auren ta
A wani bidiyo da ya sanya a shafin sa na TikTok, matashin ya kaɗu matuƙa da abinda idanuwan sa suka gane masa.
Yana buɗe asusun sai yayi arba da tulin ƴan naira dubu birjik a ciki, hakan ya sanya shi yin ihun jindaɗi.
Matashin ya kuma shawarci mutane da su koyi ɗabi’ar yin tanadi ko domin su ma su ji daɗi da farin ciki kamar yadda ya ji.
A kalamansa:
“Na fara tara waɗannan kuɗin ne a ranar 19 ga watan Janairun 2021. Ba domin babban bankin Najeriya (CBN) yace zai sauya kuɗi ba, da na cigaba da ajiyar su na tsawon shekaru. Kuna gani? Ajiya ɗabi’a ce. Sai ka koyar da kan ka.”
Ku kalli bidiyon a nan
Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin da Dimokuraɗiyya ta tattaro:
skyznoble ya rubuta:
“Ka ci sa’a wata matsala babba bata auko maka ba, ba domin hakan ba da tuni ka daɗe da buɗe shi.”
@lilexgpd ya rubuta:
“Gama ƙirgawa sannan ka gaya min nawa ka samu, ta yadda zan san ko bashin nawa zan karɓa daga wajenka.
yakubunoah3 ya rubuta:
“Irin ku ne kuka sanya CBN ya kawo wannan sabon tsarin na ƙwace kuɗi a hannun mutane. Wani kasuwancin yakamata kayi ba wai ka ajiye su a akwati ba.”
@ex_kaygozito ya rubuta:
“Ka bari waɗannan kuɗin su kai sati mai zuwa a hannun ka, lokacin zaka gane cewa ashe takarda kawai ka riƙe.”
Ƙarfin Hali: An Cafke Ɓarawo Yana Ƙoƙarin Sace Janareton Kotu
An kama wani matashi dumu-dumu yana ƙoƙarin sace janareton wata kotu a jihar Ogun.
Matashin mai suna Folorunsho Olaniyan, mai shekara 28 a duniya, an kama shi hannu dumu-dumu ne yayin da yske shirin yin awon gaba da janareton kotun Ado-Odo, cikin ƙaramar hukumar Ota a jihar Ogun.
Majiyar mu ta rahoto cewa rajistaran kotun, Kareem Tolulope, shine ya cafke Olaniyan wanda ɗan asalin Ota ne.
Wata majiya ta bayyana cewa wanda ake zargin a ranar Talata, 24 ga watan Janairu, ya shiga ɗakin da ake ajiye janareton bayan ya kwance makullin ƙofar.