Wata amarya ta rigamu gidan gaskiya kwanaki kaɗan bayan an ɗaura mata aure.
Allah ya ɗauki ran amaryar ƙasa da wata ɗaya bayan an yi mata aure da mijinta.
Amaryar mai suna Hajiya Asma’u ta rasu ne a birnin Sokoto, dake a yankin Arewa maso Yamma na Najeriya. Majiyar mu ta Shafin Linda Ikeji ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sanya gwamnonin APC basu goyi bayan Osinbajo ba -Naja’atu Muhammad
Amarya Asmau da mijinta Umar Maigari Dingyadi, an ɗaura musu aure ne a ranar Asabar, 31 ga watan Disamban 2022.
Marigayiyar ta rasu ne da safiyar ranar Alhamis, 26 ga watan Janairun 2023, a jihar Sokoto.
Mijinta Umar Maigari Dingyadi, ɗa ne a wajen ministan harkokin ƴan sanda Mohammed Maigari Dingyadi.
An yi janaizarta kamar yadda addinin musulunci ya tana da.
Muna addu’ar Allah ubangiji ya jiƙanta da rahama, ya sanya haske a kabarinta, ya gafarta mata, sannan ya kyautata namu ƙarshen. Ameen summa Ameen.
An Bayyana Wasu Kyawawan Halayen Marigayi Jarumi Abdulwahab Awarwasa
Jarumi kuma furodusa a masana’antar Kannywood wanda ya rigamu gidan gaskiya, Abdulwahab Alhassan (Awarwasa), ya samu yabo daga wayen yayen sa.
Yayyen na marigayin sun bayyana shi a matsayin mutum mai ne bin duk umarni ko hanin da su ka yi masa kan wani lamari da ya taso, wanda ya shafi gida ne ko kuma waje.
Yayan sa da ya ke bi, Abdulrazak Alhassan, shi ne ya gayawa jaridar mujallar Fim, halayen ƙanin nasa bayan an kammala jana’izar ƙanin nasa a ranar Talata, 24 ga Janairun 2023, a birnin Kano.