Wani matashi ya samu sauyi sosai bayan da budurwar sa ta gaya masa cewa bata son yanayin ƙirar jikin sa.
Matashin ya samu sauyi sosai a cikin wani bidiyo da aka sanya a manhajar TikTok wanda ya nuna yadda kamannin sa yake a baya da kuma yadda kamannin sa suke a yanzu. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Wani magidanci ya siyar da gidan sa domin ginawa ɗiyarsa katafaren wajen wasa
A cikin bidiyon an nuna wasu hotuna guda biyu, ɗaya ya nuna yadda yanayin sa yake a baya, yayin da ɗayan yadda kamannin sa suke a yanzu.
Ya bayyana cewa budurwar sa ta gaya masa cewa yayi kama da wani tsohon kaka da ya daɗe a duniya. A cikin hoto na farko an ganshi sanye da kayan jami’an tsaro. Sai dai ba a tabbatar cewa ko jami’in tsaron bane.
Fuskar sa a murtuke take a hoton farko inda ya nuna ba alamar wasa. Yayin da abubuwa suka sauya a cikin hoto na biyu. Matashin ya goge yayi haske abin sa cike da alamar ƙoshi a jikin sa.
Sauyin da ya samu kamar yadda aka gani a cikin bidiyon ya sanya mutane sun tofa albarkacin bakin su a TikTok.
Wasu daga ciki sun bayyana cewa tabbas yayi tsufa a cikin hoton farko, yayin da wasu suka yaba masa kan yadda yaje ya sauya rayuwar sa.
Wani mai amfani da @godfreymwizankhat6, shine ya sanya bidiyon a TikTok.
Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin da mutane suka bayyana waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
B I G S M A L L Z Inc ya rubuta:
“Mun fahimce ta.”
@dodo ya rubuta:
“Ko da nine zai rabu da kai saboda da farko baka nuna zakayi abin arziƙi ba.”
@Gilbert Nikaccio ya rubuta:
“Ko ba komai yanzu kana kama da kawun ta. Ban zo da rigima ba oooooh”
“Kun Ji Kunya”, Wani Fasto Ya Harzuƙa Kan Masu Bayar Da Sadakar N100
A wani labarin na daban kuma, wani fasto ya caccaki mambobin cocin sa saboda suna bayar da sadaka da naira ɗari (N100)
Wani bidiyo da yake karade yanar gizo ya nuna wani fasto yana caccakar mambobin cocin sa bisa bayar da naira ɗari (N100) a matsayin sadaka.
Faston wanda ya caccaki mabiyan nasa yayi magana ne cikin harsuna biyu, turanci da Igbo a yayin da yake faɗan nasa.