Bayern Munich ta yanke shawarar ci gaba da zama tare da Thomas Tuchel kafin kakar wasa mai zuwa,Daily Post ta rawaito.
An nada Tuchel ne a ranar 10 ga watan Afrilu don maye gurbin Julian Nagelsmann.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwana Muke Bama Barci Kan ‘Yan Najeriya Da Ke Makale A Sudan – Fadar Shugaban Kasa
Tun daga wannan lokacin, tsohon kocin Chelsea ya sa ido kan ficewar Bayern daga gasar zakarun Turai a hannun Manchester City.
A ranar Asabar kuma sun rasa matsayi na daya a gasar Bundesliga a hannun Borussia Dortmund.
Duk da haka, a cewar masanin harkokin kwallon kafa Fabrizio Romano: “Bayern ba za ta canza matsayinta kan Thomas Tuchel ba, komai ya faru a Bundesliga.
“Za a shirya kasuwar canjin bazara tare da shi domin sake fara aikin a kakar wasa mai zuwa.
“Bayern za ta shagaltu a kasuwa. Sabon dan wasan gaba, babban fifiko.”
A wani labarin kuma, JAMB Ta Dage Cigaba Da Rajistar DE Bisa Wasu Dalilai
Hukumar shirya jarabawar shiga mayan makarantun gaba da sakandire ta JAMB, ta sanar da dage ci gaba da rajistar DE, wadda ta shirya rufewa ranar Alhamis, 20 ga watan Afrilu, 2023, amma ta kara da mako guda.
Hukumar ta ce yanzu haka za a ci gaba da atisayen a ranar Asabar, 6 ga watan Mayu, 2023,sakamakon lokacin yin jarabawar gama gari ta UTME 2023 da kuma aikin kidayar jama’a na kasa zai kare.
“Wannan ci gaban an yi shi ne domin a dauki nauyin gudanar da jarabawar UTME, wadda aka sanya wa hannu za a fara ranar Talata 25 ga watan Afrilu, 2023, kuma za ta kare ranar Laraba 3 ga watan Mayu, 2023, yayin da ake shirin fara kidayar jama’a a ranar Laraba 3 ga watan Mayu, 2023, kuma za’a kammala ranar Juma’a, 5 ga watan Mayu, 2023,”
Hukumar ta bayyana hakanne a cikin wata sanarwa,a ranar Lahadi, ta hannun mai magana da yawunta, Fabian Benjamin.
Sanarwar ta ce: “Saboda haka, an umurci ‘yan takarar da ke son yin rajista don aikin DE don tabbatar da cewa sun sami DE ePINs daga wuraren sayar da kayayyaki da aka keɓe a ko kafin 30 ga watan Afrilu, 2023, lokacin da za a rufe sayar da ePIN. Ana sa ran ‘yan takarar za su wuce ofishin hukumar daga ranar Asabar, 6 ga watan Afrilu, 2023, zuwa ranar Asabar, 13 ga watan Mayu, 2023, don kammala aikin rajistar su.”