Babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a na shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu a ranar Lahadi ya bayyana cewa fadar shugaban kasa ta damu da dubban ‘yan kasarta da suka makale a kasar Sudan mai fama da tashe-tashen hankula sakamakon hatsarin da ke tattare da safarar jiragen sama a kasar da ke arewacin Afirka.
Da yake magana kan lamarin ta shafinsa na Twitter, Shehu ya rubuta cewa: “Gwamnatin Najeriya ta kasance tana shafe tsawon dare babu barci sakamakon rikicin da ake fama da shi a Sudan.
KARANTA WANNAN LABARIN: JAMB Ta Dage Cigaba Da Rajistar DE Bisa Wasu Dalilai
“Jami’anmu suna yin abubuwa da yawa, tare da yin hadin gwiwa da ofishin jakadanci a Khartoum, gwamnatocin Sudan da Habasha suna kokarin tabbatar da tsaron dimbin ‘yan kasarmu a can.
“Ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama wanda ke gudanar da wadannan yunƙurin yana da kwarin gwiwar cewa za su fara jigilar mutane zuwa ga tsaro da wuri.
“Kalli Ministan ya bayyana abin da suke yi a Channels TV da yammacin yau.”
Rikicin da ya barke tsakanin dakarun Sudan da kungiyar Rapid Support Force, ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 400 tare da jikkata kusan 3,500.
Rikicin ya kuma raba dubban fararen hula da suka tsere daga Khartoum babban birnin kasar, yayin da rikicin da ya fara a ranar 8 ga watan Afrilu ya shiga kwana na 15 a ranar Lahadi.
Har ya zuwa kwanan nan, sojojin Sudan karkashin jagorancin Janar Abdel al-Burhan, da kuma kungiyar sa kai ta RSF, karkashin jagorancin Janar Mohamed Dagalo, sun kasance kawaye.
Sun yi aiki tare a shekara ta 2019 a wani boren al’ummar kasar da ya hambarar da mulkin kama-karya na Omar al-Bashir, wanda ya mulki kasar tsawon shekaru talatin.
A wani labarin kuma, Bamu Da Bukatar Kwankwaso a APC – Dan Bilki Kwamanda
Jigo a jam’iyyar APC a jihar Kano, Abdulmajeed Danbiliki Kwamanda ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta bukatar tsohon gwamnan jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.
Wannan bayani ya fito ne a matsayin martani ga yunkurin Sanata Kwankwaso na komawa APC.
Comments 1