Wani bene mai hawa biyar ya rushe a layin Ladipo Oluwole Street, cikin GRA, a yankin Apapa na jihar Legas.
Benen wanda yanzu ake ginin sa ya ruguje ne bayan an yi wata tsawa.
Jami’an hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas (LASBCA) tuni har sun zagaye benen. Jaridar The Cable ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: JAMB Ta Dage Cigaba Da Rajistar DE Bisa Wasu Dalilai
Wani ɗan balantiya a ofishin jami’an hukumar Nigerian Security and Civil Defence Corp (NSCDC) na Ajeromi Ifelodun LCDA, Asimiyu Tiamiyu, ya ce ba a samu asarar rai ba.
Ya bayyana cewa babu ma’aikata a lokacim da lamarin ya auku, inda ya ƙara da cewa dole ne gwamnatin jihar ta ƙara matsi ƙaimi wajen hana aukuwar yawaitar ruguje-rugujen gine-gine a jihar.
Lamarin ya auku ne kwanaki 10 bayan wani bene mai hawa 7 ya ruguje a yankin Banana Island na jihar.
Jami’an NDLEA Sun Cafke Wasu Masu Zuwa Umrah Dauke Da Miyagun Kwayoyi
Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) sun cafke wani bazawari mai suna Ariyibi Ahmed Olaseinde da wata mata da ta rabu da mijinta mai suna Akanbi Silifat Tunrayo, suna kan hanyar su ta zuwa ƙasa mai tsarki yin aikin Umrah
Jami’an na hukumar sun cafke mutanen biyu a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke a Ikeja jihar Legas, ɗauke da kilogiram 14.4 na hodar iblis d aka sanya cikin atamfa da leshe.