Dan wasan tsakiya na Manchester City, Bernardo Silva, yana gab da komawa Barcelona a bazara.
An alakanta Silva da komawa Barcelona na dan wani lokaci, amma rashin issasun kudade daga kungiyar Catalan sun tsayar da yarjejeniyar.
Sai dai Barcelona ta gaiyaci wani masani kan farfado da tattalin arziki, wanda ya basu shawarar neman Lamuni domin warware matsalar durkushewar tattalin arziki da suka shiga.
A cewar jaridar Catalan Sport, lamunin, wanda wani bangare ya fito daga siyar da wani sashi na kudaden da suke samu daga kafafen Talbijin na kungiyar, ya baiwa Blaugrana damar samun jarin da ake buƙata a wannan bazarar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Buni Ya Halarci Jana’izar Marigayi Goni Bukar Kwamishinan Wasanni
Rahoton ya kara da cewa, babu wata matsala da ake tsammanin za’a samu tsakanin Barcelona da Silva kan cimma yarjejeniyar komawa kungiyar domin taka leda a kakar da zamu shiga.
Silva ya taimaka wa Man City wurin lashe kofin Premier a bara.
A wani labarin kuma na daban.
Hukumar EFCC ta kama mutane 17 da ake zargi da damfara ta yanar gizo a Legas
Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC shiyyar Legas sun kama wasu mutane 17 da ake zargi da damfarar yanar gizo a jihar ta Legas.
An kama wadanda ake zargin ne a wani samame da suka kai a Kay-Farm Estate, Ishaga a jihar Legas, biyo bayan wasu bayanan sirri da aka samu kan ayyukan mambobin wata kungiyar masu aikata laifuka ta Intanet da ke damfarar intanet.
An bayyana sunayen wadanda aka kama kamar haka Ogunnowo Aderosola, Adebesin Adeyinka, Nkeokelonye Stanley Ifeanyi, Afolabi Babatunde Oluwaseun, Onyeka Nwokoro, Micheal Adedayo Owolabi, Musah Esosa Hakeem, Osim Happiness, Sanusi Timilehin Olawale, Sanusi Timilehin Rasak, Emmanuel Obogo Adeja, Ogunshoni Samuel Osa Eni Owola , Alabi Ajekola Peter, Timilehin Damilola Emmanuel, Egbuno Ifeanyi Favor da Jimoh Oluwapelumi Ibrahim.
Sanarwar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta fitar a shafinta na Twitter ta ce an gano wasu kayayyaki kamar motoci, na’urorin hannu, da kwamfyutocin tafi da gidanka bayan kama su.
Ya kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gabab kotu bayan an kammala bincike