Wani ƙayataccen bidiyo na wata kyakkyawar soja wanda ya nuna tsananin kyawunta a cikin khakin ta na soja, ya ɗauki hankulan mutane sosai.
Sojan tana da wata baiwa ta musamman ta jan hankali kamar yadda ta yi a cikin ɗan gajeran bidiyon wanda ya karaɗe manhajar TikTok. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Ana gobe sallah, hukumar DSS ta kama muggan makamai a jihar Kano
Mutane da dama ƴan soshiyal midiya da suka kalli bidiyon, sun lura da kyau irin wanda sojan ta ke da shi, inda suka ware lokacin su wajen kwararo mata kalaman yabawa da kyawun da ta ke da shi.
Bidiyon ya yadu sosai a manhajar TikTok, inda mutane suka yi ta tofa albarkacin bakin su a kansa. Ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, sama da mutum dubu casa’in ne suka danna masa alamar ‘like’ yayin da sama da mutum dubu ɗaya (1000) suka yi sharhi a kansa.
Ku kalli bidiyon a nan
Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin da mutane suka bayyana akan bidiyon, waɗanda Dimokuraɗiyya ta tattaro:
@ruthmoses363 ta rubuta:
“Kina da kyau sosai”
@uhiomuchennaemman commented:
“Kin yi kyau sosai.”
@sugarpinopino ya rubuta:
“Kin yi kyau sosai masoyiya.”
@Y9lac ya rubuta:
“Allah ya kare ki. Wow kon haɗu iya haɗuwa.”
@Hashimu901 ya rubuta:
“Ina son ki, ina ƙaunar ki soja.”
I like u, I love u Soldier”
@user930314953190 ya rubuta:
“Shaiil! kalli wata kyakkyawar budurwa oooe.”
Bidiyon Wasu Kyawawan Sojoji Suna Tikar Rawa Ya Dauki Hankula
Wani ɗan gajeran bidiyo mai ƙayatarwa na wasu sojoji mata gudu uku suna tiƙar rawa ya janyo cece-kuce manhajar TikTok.
A cikin bidiyon kyawawan sojojin sun yi kalar rawa iri daban-daban waɗanda suka yi su cikin ƙwarewa