A yayin da ake cigaba da ƙarancin sababbin kuɗin naira, wani bidiyo da wani mai amfani da sunan @zitanne_fashion a manhajar TikTok ya sanya, ya nuna wata mata ɗauke da sababbin kuɗin masu yawa.
Matar wacce ba a nuna fuskarta a cikin bidiyon ba, tana siyar da kuɗin ne domin ta samu riba. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Tsoho ya tayar da rigima a banki bayan an hana shi cirar kuɗi
Ta gayawa mutane cewa sai dai su biya naira dubu sittin (N60,000) a basu naira dubu hamsin (N50,000) na sababbin kuɗin. Hakan na nufin a duk dubu hamsin na sababbin kuɗin zata ci ribar naira dubu goma.
Mutane sun yi ta mamaki yadda aka yi har wata mai talla ta samu sababbin kuɗin, yayin da mutane da dama suka kasa samu a bankuna.
Duk da cewa dai matar bata cika ribar ba sosai, amma irin su sune babban maƙasuɗin da ya sanya mutane ba su samun kuɗin a bankunan su.
Ku kalli bidiyon a nan
Mutane da dama sun yi sharhi akan wannan bidiyon na mai siyar da kuɗin, inda suka bayyana mabanbantan ra’ayoyi.
Ga kaɗan daga cikin waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
TemiMoney ta rubuta:
“Har tana da tsaurin idon da zata ce guda nawa kake so.”
Prince T ya rubuta:
“Wanene yake siyar mu su da wannan kuɗin? Shin ba manajan banki bane.”
Munachimso ya rubuta:
“Wani mutum ya biya dubu ɗari ya karɓi miliyan ɗaya.”
Mathias Annys ya rubuta:
“Wace ƙasa ce ke siyar da kuɗinta da kuɗin ƙasar? Wannan hauka ne.”
Ma’aikatan Banki Sun Tsere Ta Katanga Bayan Mutane Sun Ritsa Su a Banki
A wani labarin na daban kuma, wasu ma’aikatan banki sun tsere ta katanga bayan mutane sun ritsa su a banki.
Wani bidiyo da aka ɗauka ya nuna ma’aikatan wani banki na tserewa daga wajen aikin su ta katangar baya, yayin da mutane suka kewaye harabar bankin a ƙoƙarin su na samun kuɗin su.
Wannan na zuwa ne yayin da babban bankin Najeriya (CBN) ya haƙiƙance cewa ranar 10 ga watan Fabrairu itace ranar ƙarshe na musanya tsofaffin kuɗi da sababbi.