Bidiyon wani tsoho a fusace cikin banki ya bayyana, wanda ya nuna yadda aka ƙi bashi dama ya cira kuɗinsa a cikin wani banki.
Ga dukkan alamu, sabon tsarin babban bankin Najeriya na bayar da kuɗi ƴan kaɗan shine ya ritsa da tsohon.
Bidiyon wanda wani mai amfani da sunan @mirianchinagorom52, ya sanya a TikTok ya nuna tsohon a fusace a cikin harabar bankin. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Tirƙashi: Bidiyon wata budurwa mai aski da falleliyar wuƙa ya ɗauki hankula
Tsohon yana ta rigima da caccakar ma’aikatan bankin, waɗanda ya zarga da hana shi kuɗin sa waɗanda suke mallakin sa ne.
A cewar sa, a shekarun da yake da su, ma’aikatan bankin suyi addu’ar su daɗe a duniya kamar yadda yayi. Yace shekarar sa 82 a duniya, sannan kuma tun shekakar 1974 yake amfani da banki.
Tun lokacin da wannan sabon tsarin na CBN na hana kuɗi yawo a hannun mutane, ƴan Najeriya na shan baƙar wahala wajen samun kuɗi domin biyan buƙatun su na yau da kullum.
A yayin da sababbin takardun kuɗin suka yi ƙaranci, masu sana’ar PoS kuma sun ƙara yawan kuɗin da suke karɓa a hannun mutane, wanda hakan ya sanya matsalar ta ƙara girmama.
Ku kalli bidiyon a nan
Elon Musk Ya Farfaɗo, Yana Dab Da Komawa Matsayin Attajirin Da Yafi Kowa Kuɗi
A wani labarin na daban kuma, attajirin da yafi kowa kuɗi a duniya a baya, ya fara farfaɗowa inda yanzu yake dab da komawa matsayin sa.
Elon Musk a ranar Litinin 6 ga watan Fabrairun 2023, ya samu $3.9bn (N1.81trn) wanda hakan ya sanya samu N4.45trn ($9.8 billion) a mako guda.
Kuɗin da Elon Musk ya samu a ranar Litinin sun fi gabaɗaya kasafin kuɗin N1.76trn na shekarar 2023 na jihar Legas.