Wani bidiyo da aka ɗauka ya nuna ma’aikatan wani banki na tserewa daga wajen aikin su ta katangar baya, yayin da mutane suka kewaye harabar bankin a ƙoƙarin su na samun kuɗin su.
Wannan na zuwa ne yayin da babban bankin Najeriya (CBN) ya haƙiƙance cewa ranar 10 ga watan Fabrairu itace ranar ƙarshe na musanya tsofaffin kuɗi da sababbi.
KU KARANTA KUMA: Tirƙashi: Bidiyon wata budurwa mai aski da falleliyar wuƙa ya ɗauki hankula
A dalilin wannan sabon tsarin na CBN, miliyoyin ƴan Najeriya na ji a jika inda wahalalu masu ɗumbin yawa suka ƙaru a gare su.
A cikin bidiyon an nuna ma’aikatan bankin na haurawa ta katanga domin gujewa mutane. An jiyo ɗaya daga cikin su nayin waya inda yake tambayar ko ƴan sanda sun ƙaraso wajen.
Ku kalli bidiyon a nan
A halin da ake ciki, bidiyon ya sanya ƴan Najeriya tafka mahawara sosai a kafafen sada zumunta.
Ga kaɗan daga cikin maganganun da mutane suka yi akan bidiyon, waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
Alasela Kehinde:
“Na yi tunanin akwai mutanen dake goyon bayan wannan tsarin inda suke cewa an yi shine domin a murƙushe ƴan siyasa, ƴan siyasa nawa suka gani a layin ATM ko suke roƙon a basu sababbin kuɗi.”
“Talakawa sune suke shan wahalar sa. Yakamata Emefiele ya dakata da wannan mugun tsarin ko kuma a cire shi daga muƙamin sa.”
Adegoke Baiyere:
“Ta yaya muka yiwa Buhari da APC laifi da har suka ƙaƙaba mana wannan muguntar? Waɗannan fa ƴan Najeriya ne waɗanda ba su ji ba basu gani ba.”
Jessica Ibrahim:
“Wannan abin takaici ne kamar yadda bankin Zenith ko da yaushe suke cewa basu da kuɗi a ATM sannan kuma idan an tura basu tafiya.
Tsoho Ya Tayar Da Rigima Cikin Banki Bayan An Hana Shi Cirar Kuɗi
A wani labarin na daban kuma, wani tsoho ya tayar da ƙura a cikin banki bayan an hana shi ciro ƴan kuɗaɗen sa.
Bidiyon wani tsoho a fusace cikin banki ya bayyana, wanda ya nuna yadda aka ƙi bashi dama ya cira kuɗinsa a cikin wani banki.
Ga dukkan alamu, sabon tsarin babban bankin Najeriya na bayar da kuɗi ƴan kaɗan shine ya ritsa da tsohon.