Wata budurwa ƴar Najeriya mai lallurar in’ina ta koka kan yadda samun saurayin da zai yi soyayya da ita, ya zame mata wani gagarumin aiki mai matuƙar wahala.
Wani mai yin bidiyoyi a TikTok mai suna Theo Ayomoh, wanda ya nunawa masu bibiyarsa budurwar ya bayyana cewa ba namijin da yake son yayi soyayya da ita saboda tana yin in’ina. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Tirƙashi: An ritsa fasto ɗauke da kororon roba yana tsaka da wa’azi
A cewar budurwar, ta gaji da gudun da samari suke yi mata.
“Samari gudu na suke yi saboda yadda nake yin magana, hakan babban ƙalubale ne a gare ni.”
Budurwar wacce ƴar kasuwa ce ta bayyana cewa har yanzu bata cire tsammanin samun wanda zai so ta ba, amma dai tana son namijin da baya yin in’ina kamar ta.
Mutane da yawa sun tausaya mata kan wannan ƙalubalen da take fuskanta, inda da yawa daga ciki suka ƙarfafa mata guiwa.
Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin da mutane suka bayyana waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
ogerenyasamson ya rubuta: ‘
“Kiyi haƙuri ƴanmata sannan kina da kyau, da ba domin ban isa aure ba da nayi wuff dake.”
joshuamoseskargbo ya rubuta:
“Kada ki damu kan ki, ba laifin ki bane haka Allah ya halicce ta.”
Tracy ta rubuta:
“Ƴanmata na tausaya miki kan halin da kike ciki amma ina da wani ɗan’uwa idan kina son shi.”
user9767425305312 ya rubuta:
”Hawaye sun cika min idona. Kawai ta riƙa faɗin duk abinda take son faɗi a zuciya kafin ta furta shi, hakan zai taimaka mata ta rage in’ina.”
Yadda Nayi Wuff Da Kyakkyawar Budurwa a Yanar Gizo -Wani Matashi
A wani labarin na daban kuma, wani matashi baƙar fata ya bayyana hanyar da ya bi yayi wuff da wata kyakkyawar baturiya.
Wani ƙayataccen bidiyo ya nuna wani matashi yana shan soyayya da wata kyakkyawar baturiya.
A cikin bidiyon wanda wani mai amfani da sunan @cyprianandsarah a manhajar TikTok ya sanya, matashin ya bayyana cewa ya haɗu da masoyiyar tasa ne a Instagram.