Wani magidanci ɗan Najeriya ya ce ga garin ku nan bayan ya gano cewa matar sa, da ya ɗauki nauyin ta zuwa ƙasar waje domin samun ingantacciyar rayuwa, ta bari wani ya ɗirka mata ciki.
A cewar wani mai amfani da sunan @BolanleCole a manhajar Twitter, wanda ya sanya labarin, magidancin ya sha wuya kafin ya samu ya tura matar sa da ƴaƴan su biyu zuwa ƙasar Burtaniya, domin su samu rayuwa mai kyau, ya yin da shi kuma ya tsaya a nan Najeriya. Shafin Yabaleftoneline ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Al-Nassr Na Shirin Daukan Abokin Wasan Ronaldo A Man United
Abin takaicin, matar tana zuwa can ƙasar kawai sai ta fara sheƙe ayar ta kawai abin ta, inda daga ƙarshe ta samu juna biyu, wanda mijin na ta bai san da shi ba sai kwanan nan.
Bolanle Cole bayyana cewa jin labarin cewa matar sa ta samu juna biyu, ya sanya magidancin jin cewa ba zai iya jurewa ba, ya sanya ya mutu.
A kalamansa:
“Wani magidanci ya ƙure kan sa ya tura matar sa da ƴaƴan sa biyu zuwa birnin Liverpool a UK domin samun rayuwa mai kyau, amma sai matar ta fara bin wani namiji daban har sai da yayi mata ciki. Mijin ta na Najeriya bai sani ba har sai da ta haihu, tsananin kaɗuwar da ya yi saboda jin labarin ya yi sanadiyyar ajalin sa. Abubuwa na faruwa a duniyar nan.”
“Nayi Nadama”, Wata Matar Aure Ta So Yin Wayon Hakimi, Abubuwa Sun Kwabe Mata
Wata mata ta koma neman shawara da taimako domin a halin yanzu tana dab da rasa dukkanin kadarorin ta.
A cewar ta, ta siya kadarori a asirce waɗanda ta sanya sunan ɗan’uwanta a takardun, domin tsoron cewa mijinta zai iya sakin ta ya nemi ya kwace kadarorin