Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake Kasar Birtaniya sun tsallake rijiya da baya bayan da suka samu damar zuwa gasar zakarun turai na baɗi.
A yau Lahadi ne aka karkare wasannin gasar Firimiya ta Kasar Ingila bayan shafe makonni talatin da takwas ana gumurzu.
Nasarar da Tottenham ta yi a kan Leicester City uta ta baiwa Chelsea damar tsallakewa zuwa gasar na ta baɗi da tazarar kwallaye uku kachala.
Ko da yake Chelsean ta yi rashin nasara a kan Aston Villa, amma hakan bai hana dakarun Thomas Tuchel ɗin samu damar shiga cikin hudun farko da za su wakilci Ingila a gasar ta badi ba.
Ita kuwa Liverpool dukan da ta yi wa Crystal Palace 2:0 shine damarta ta karshe da ta samu ta zuwa gasar bayan da ta karkare a mataki na uku a gasar ta Firimiya.
Yanzu haka Manchester City da ta lashe kofin Firimiyar da Manchester United da Liverpool da Chelsea ne za su wakilci Ingila a gasar ta badi, wadanda da ma su ne suka wakilce ta a bara.