Ma’aikatar Harkokin Lafiya ta Kasar Saudiyya ta sanar da cewa mutane dubu sittin ne kachal za su gudanar Ibadar aikin hajjin bana daga ciki da wajen kasar.
Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin na tuwita, ta ce kuma muddin mutum ya wuce shekara ko kuma bai kai shekara takwas ba, sannan kuma bai kwanta a asibiti ba daga watanni shida da suka wuce, to babu makawa aikin hajjin na bana ya wce shi kenan.
Kazalika sanarwar ta ce indai mutum ba a yi mishi rigafin Korona na farko da na biyu ba to ba za a yi aikin na bana da shi ba, domin dole ne ya gabatar da takardar shaidar cewa an yi mishi rigafin.
Har wa yau ta ce rigafin dole ya zama cewa na daga cikin rigafin da kasar Saudiyya ta yi amanna da shi.
Baya ga nan kuma sanarwa ta ce duk maniyyaci da ya isa kasar dole ne a killace shi na kwana uku daga zarr sun sauka.
Daga karshe sanarwr ta ce sanya takunkumi da kuma bada tazara yayin mu’amala ya zama wajibi, domin ta haka ne kaɗai za a kiyaye bazuwar annobar korona.