Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake kasar Birtaniya ta bude kofar tattaunawa da Sevilla don dauko dan wasan byanta Jules Kounde.
Har kawo yanzu dai kociya Thomas Tuchel bai kara kowane dan wasa a tawagarsa da ta lashe gasar zakarun Turai ba, sai dai Jaridar Guardian ta yi amannar cewa komai ka iya canjawa.
Yanzu haka ana ganin dai Kounde ka iya kara gishiri ga tawagar bayan Chelsea, ko da yake har yanzu tattaunawa ba ta yi nisa ba kasancewar ba lallai ba ne Chelsea ta iya biyan Pam miliyan 68 da Sevilla ke nema.
Da ma dai baya ga Chelsea ita ma Manchester United ta kwallafa ranta kan dan wasan, wanda ana ganin nan ma zai iya karfafa tawagar Ole Gunner Soljsker.
Siyo Raphael Varane daga Real Madrid ka iya kara karfin gwiwa wa jama’a cewa United za ta iya daukar Kounde kasancewar su yan kasa daya.