Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa da dangogin su ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye, ya ce yawan cin hanci da rashawa ne ke kara haddasa rashin tsaro a kasar nan. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a yayin da ake fara taron yini biyu na kwamitin majalisar wakilai kan yaki da cin hanci da rashawa da cibiyar nazarin harkokin dokoki da dimokaradiyya ta kasa (NILDS) da KAS suka shirya a Abuja.
KARANTA WANNAN LAVARIN: Gwamna Ganduje Ya Bude Cibiyar Kula Da Masu Cutar Tamowa
Owasanoye ya ce cin hanci da rashawa na ciwa Najeriya tuwo a kwarya, don haka dole ne a tunkare shi a yi maganinsa sosai domin samun kwanciyar hankali da zaman lafiya a kasar nan.
Ya kuma zargi wasu ‘yan majalisar dokokin kasar nan da manyan hafsoshin soji da cin hanci da rashawa, ya kuma bukaci su kaurace wa ayyukan da ke haifar da rashin tsaro.
Ya ce, “Rashin shugabanci, cin hanci da rashawa da rugujewar doka na haifar da rashin tsaro. Manyan hafsoshin soji na karkatar da kudaden da ake warewa bangaren tsaro a cikin aljihunsu na kashin kansu, don haka, hakan yana haifar da rashin tsaro.
“Amfani da kudaden da aka ware domin tsaro don wasu dalilai kamar biyan ƴan daba ga ayyukan laifi ga ’yan siyasa, da dai sauransu.
Anashi bangaren Darakta Janar na NILDS, Farfesa Sulaiman Abubakar ya ce, “Yayin da kuka yi la’akari da yadda cin hanci da rashawa ke kawo cikas ga tsaro da ci gaban bil’adama, ina fatan wannan kwamiti zai ci gaba da karfafa dangantakarsa da hukumomin yaki da rashawa da kuma yin amfani da matakan doka don kara kaimi..”
Daga cikin wadanda suka halarci taron, akwai; Shehu Garba, shugaban kwamitin majalisar wakilai kan yaki da cin hanci da rashawa, mataimakin shugaban masu rinjaye, Peter Akpatason da wasu da dama.
A WANI LABARI KUMA: Zamfara: PDP Ta Zaɓi Ranar Sake Zaɓen Fidda Gwanin Yan Takarar Gwamna
Jam’iyyar PDP a jihar Zamfara ta sanya ranar Juma’a (gobe) domin sake gudanar da zaben fidda gwani na takarar gwamna a jihar.
A ranar Juma’ar da ta gabata, wata babbar kotun tarayya a jihar ta soke zaben fidda gwani na takarar gwamna na jam’iyyar da Alhaji Dauda Lawal Dare wanda ya lashe zaben fidda gwanin.